Mulkin Buhari Annoba Ce Ga Mutanen Najeriya - Solomon Dalung Tsohon Ministan wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana jimamin sa kan kashe-kashen da ake yi a yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya da Arewa Maso Yamma. Dalung, ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo a shafinsa na Facebook inda ya bayyana bakin cikin shi game da yadda ake kashe ‘yan kasa a yankin Arewa duk da tsananin kashe kudin tsaro. Dalung yace an kashe yawancin yan Najeriya mazauna Arewa a karkashin kulawar Buhari fiye da kowane lokaci a cikin tarihi. Da yake magana da yaren Hausa, Dalung, wanda ya kasance minista a karkashin Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2019, ya bayyana tsarin mulkin a matsayin wanda ya gaza. Talla Ya soki Shugaban kasar da laifin kyale jami’an tsaro su kwashe dukiyar al’umma ba tare da sakamako mai gamsarwa ba. Ya ce, “Ya Shugaba, ka ba wadannan mutane karin kudi, duk da haka muna ci gaba da asarar rayuka da dama. Wadannan mutane suna wadatar da ...
Labaran Duniya, Sharhin al'amuran yau da kullum, Siyasa, Kimiyya, Ilimantarwa da Nishadantarwa