Skip to main content


Mulkin Buhari Annoba Ce Ga Mutanen Najeriya - Solomon Dalung


Tsohon Ministan wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana jimamin sa kan kashe-kashen da ake yi a yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya da Arewa Maso Yamma.

Dalung, ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo a shafinsa na Facebook inda ya bayyana bakin cikin shi game da yadda ake kashe ‘yan kasa a yankin Arewa duk da tsananin kashe kudin tsaro.

Dalung yace an kashe yawancin yan Najeriya mazauna Arewa a karkashin kulawar Buhari fiye da kowane lokaci a cikin tarihi.

Da yake magana da yaren Hausa, Dalung, wanda ya kasance minista a karkashin Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2019, ya bayyana tsarin mulkin a matsayin wanda ya gaza.
          Talla


Ya soki Shugaban kasar da laifin kyale jami’an tsaro su kwashe dukiyar al’umma ba tare da sakamako mai gamsarwa ba.

Ya ce, “Ya Shugaba, ka ba wadannan mutane karin kudi, duk da haka muna ci gaba da asarar rayuka da dama.

Wadannan mutane suna wadatar da kansu ne kawai da kudaden jama’a.

Abin bakin ciki, wani lokaci daya wuce ka ambata cewa sun ki bin umarninka; Ina nufin umarnin Kwamandan-In-Chief, don haka me ya sa har yanzu kake hakuri da su?

Shugaban kasa, lokaci ya yi da ka kyale su, saboda ci gaba da kasancewa a cikin su yana lalata tsarinka ne kawai.

Ni ba annabi bane amma zan iya yin hasashen cewa idan ba a dauki wani mataki akan wadannan masu cin amana a cikin gwamnatin ka ba, zaka yi nadama sosai a shekarar 2021.

Daga Borno zuwa Kwara, daga Filato zuwa Sokoto, rayuwar dan Adam ta zama mai sauki fiye da na kaza.

Misali, yadda rayukan mutanen da ba su ji ba su gani ba ke halaka, a kowane lokacin, kuma a garinka na jihar Katsina.” a cewar Dalung









Comments

Popular posts from this blog

TAJBank: Empowering Lives Through Non-Interest Banking

TAJBank: Empowering Lives Through Non-Interest Banking By Sani Ahmad Giwa   In a world where many financial institutions are driven by profit at the expense of their customers, TAJBank stands tall as a beacon of trust, integrity, and innovation. TAJBank is not just another bank — it is a movement toward ethical prosperity, financial inclusion, and peace of mind. If you’re searching for a banking partner that truly cares about your growth, your values, and your future — TAJBank is the answer. Why TAJBank? Because You Deserve Better Here’s why thousands of Nigerians across the country are making the switch to TAJBank: ✅ Non-Interest Banking (Riba-Free): TAJBank operates on Islamic finance principles, meaning no interest is charged or paid. Your money works for you in a way that’s ethical, fair, and transparent — without hidden fees or exploitative charges. ✅ Ethics First: At the core of TAJBank is a strong moral foundation. This is a bank that honors honesty, transparency, and mutual...
Tsaro: Za A Yi Zanga-Zanga A Arewacin Najeriya Kungiyar matasan Arewa karkashin jagorancin Alhaji Nastura Ahmad Shariff ta kira jama’ar arewacin Najeriya su fito suyi zanga zanga akan matsalar tsaro da ta addabi yankin a ranar Talata. Za a yi wannan zanga zanga ne a dukkanin jihohi goma sha tara na arewacin Najeriyar. Zanga zangar za ta kunshi kungiyoyin yan gwagwarmaya na farar hulla, kana za a watsa ta a kafafen sada zumunta. A baya bayan nan kuma dai harkar tsaro ta yi matukar gurbacewa a yankin Arewacin Najeriya musamman a jihohin Katsina, Sokoto da kuma Zamfara.
DOKAR FYADE: BA NAN GIZO KE SAKA BA Daga Sani Ahmad Giwa Fyade dai a Najeriya tun ba yau ba ya zama ruwan dare gauraye duniya, wanda kuma hukuma suka kasa daukan wani tsauraran matakai ga duk wanda ya aikata hakan akan kananan yara ko manya; inda lokuta da dama har wasu kungiyoyi ko masu hannu da shuni suke bai wa mutanen da suke aikata laifin fyade kariya ta hanyar daukar lauyoyi da makamantansu. Hakika wannan dabi'a ta sa guyawun iyayen yaran da aka lalata wa rayuwa yin sanyi wajen bin diddigin kwatar wa 'ya'yansu hakkinsu, haka suke hakura suna kai kokensu wajen Allah. Madallah da irin kokarin da majalisar dokokin kasa da na wasu jihohi suke yi na himmar samar da wata doka da za ta iya rage yawaitar wannan dabi'a ta fyade, kuma za ta tsoratar tare da razanar da masu sha'awar aikata hakan ga kananan yara ko manya. Kamar yadda yawancin membobin majalisar suka fi raja'a akan shi shi ne a zartas da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu cikakkiyar shaid...