JIBWIS Ta Yi Allah Wadai Da Kashe-Kashen Da 'Yan Ta'adda Ke Yi A Yankin Arewa.
Kungiyar ta kuma umurci limaman juma'a da kamsul-salawat da suyi addu'oi a masallatai
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Kungiyar wa'azin musulunci ta JIBWIS ta nuna alhininta da matukar damuwa akan kashe-kashen bayin Allah da basuji ba, basu gani ba da ake yi a Jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Borno da sauran su.
Hakan ya fito ne daga bakin Shugaban JIBWIS Sheik (Dr) Abdullahi Bala Lau a wani zantawa da yayi da 'yan jaridu a maraicen asabar dinnan.
Shehin Malamin ya nuna damuwarsa matuka akan kisan kiyashi da ake yi a yankin arewa maso gabar, da arewa maso yamma, ''Ina mika sako na musanman ga Gwammatin tarayya cewa wannan kashe-kashen da ake yi fa yayi yawa, koda rai guda ne wajibine Gwannati ta kare ballantana rayukan mutane masu yawa.
Dole Gwamnati ta sake nazari domin tsare rayukan Jama'arta, tun mutane basu fara daukan makami domin kare kansu ba, wanda a karshe ana iya samun wata matsala idan mutane suka mallaki makamai a hannuwansu, Inji shi"
Shugaban na IZALA yaci gaba da cewa, Kiyaye rayukan mutane wajibine akan Gwamnati, domin da kiyaye rayuwar su ne za su ci gaba da yiwa Gwannati biyayya.
Ka'ida ce a cikin Al-Qur'ani, bayan Allah ya zaunar da Quraishawa lafiya kuma ya basu arziki sai ya ce musu:
ﻓﻠﻴﻌﺒﺪﻭﭐ ﺭﺏ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺒﻴﺖ
"Su bautawa Ubangijin wannan gida"
ﺍﻟﺬﻱ ﺃﻃﻌﻤﻬﻢ ﻣﻦ ﺟﻮﻉ ﻭﺀﺍﻣﻨﻬﻢ ﻣﻦ ﺧﻮﻑ *
"Wanda ya ciyar da su daga yunwa kuma ya amintar da su daga tsoro."
Saboda haka idan Allah zai bukaci Quraishawa su bauta masa saboda ya zaunar da su lafiya to, haka idan Gwamnati tana son 'yan kasarta su rika mata biyayya dari bisa dari, ta samar musu da zaman lafiya a garuruwan su.
Sheik Bala Lau ya ja hankalin Jami'an tsaro da su sani amanar 'Yan Nigeria ce Shugaban kasa ya saka su su wakilce shi, cin amana ne rashin tsayawa a kula da rayukan Jama'ah. Saboda haka wannan Kungiya ta IZALA tana kira da babban murya ga Jami'an tsaro da su kara daukan mataki domin tsare rayukan Jama'ah.
Daga karshen karshe, shugaban ya umurci Shugabannin JIBWIS na jihohi da kananan hukumomi musamman Malamai da Limamai a duk fadin Naijeriya da su lazimci addu'o'i akan Allah ya kawo mana karshen wadannan kashe kashen. Idan mu kayi wannan muna fatan zamu samu sauki daga Allah.
A karshe yace wannan Kungiya tana kara kira ga 'Yan Nigeria da su sani cewa babu abinda addu'a bata yi, mu dage da addu'a akan Allah ya zaunar damu lafiya, wadanda suka hada kai domin su yaki kasar nan Allah ya san su, Allah yayi mana maganinsu. Sannan mu yawaita tuba da Istigfari


Comments
Post a Comment