CORONA: BANKIN CBN YA WARE NAIRA BILYAN HAMSIN DOMIN TALLAFAWA MUTANE - Lai Mohammed
Daga Sumayya Bashir
Ministan yada labarai Mista Lai Mohammed ya ce babban bankin Najeriya CBN ya ware zunzurutun kudade har naira bilyan 50 domin tallafawa wadanda annobar cutar Corona ta tagayyara ta fuskar durkushewar kasuwancinsu, da kuma magidantan da suke cikin halin ha-ula'i.
Lai Mohammed ya ce tuni dai bankin ya fara turawa da kudaden ta hanyar bankin 'yan kasuwa wato NIRSAL wanda ya dauki ragamar aikin don ganin an ba mutanen da suka dace, musamman kananan 'yan kasuwa da magidanta.

Comments
Post a Comment