DOKAR FYADE: BA NAN GIZO KE SAKA BA
Daga Sani Ahmad Giwa
Fyade dai a Najeriya tun ba yau ba ya zama ruwan dare gauraye duniya, wanda kuma hukuma suka kasa daukan wani tsauraran matakai ga duk wanda ya aikata hakan akan kananan yara ko manya; inda lokuta da dama har wasu kungiyoyi ko masu hannu da shuni suke bai wa mutanen da suke aikata laifin fyade kariya ta hanyar daukar lauyoyi da makamantansu.
Hakika wannan dabi'a ta sa guyawun iyayen yaran da aka lalata wa rayuwa yin sanyi wajen bin diddigin kwatar wa 'ya'yansu hakkinsu, haka suke hakura suna kai kokensu wajen Allah.
Madallah da irin kokarin da majalisar dokokin kasa da na wasu jihohi suke yi na himmar samar da wata doka da za ta iya rage yawaitar wannan dabi'a ta fyade, kuma za ta tsoratar tare da razanar da masu sha'awar aikata hakan ga kananan yara ko manya. Kamar yadda yawancin membobin majalisar suka fi raja'a akan shi shi ne a zartas da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu cikakkiyar shaidar ya aikata fyaden.
Abun tambayar shi ne, shin dokar za ta yi tasiri bayan akwai sauran rina a kaba? Dalilin da ya sa na ce haka shi ne, mu dauki mas'alar Maryam Sanda wadda kotu ta yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya, ina mai tabbatar muku ko da Appeal court ta sake yanke wa Maryam hukuncin kisa ba za a kashe ta ba, domin domin tana da damar sake daukaka kara zuwa kotun daga ita sai dai Allah ya isa, kuma ko a can din idan aka yanke mata hukuncin kisa ba za a kasheta ba, sai dai ta cigaba da zaman gidan yari har zuwa lokacin da gwamnatin Najeriya za ta gyara inda matsalar take.
Shin a ina matsalar take?
Babbar matsalar ko da an saka dokar kisa ga masu aikata fyade, sai gwamnatin Najeriya ta yi gyara a sashen ma'aikatan gidajen yari, kasancewar wadanda aka dauka domin zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ko harbewa da bindiga yanzu duk sun mutu, sama da shekara ashirin da biyar har yanzu kuma gwamnati ba ta samar da wasu ba, ko kuma ba ta dauki ma'aikatan da za su dinga yin wannan aiki ba, kuma babu wanda yake da hakkin yin wannan kisa sai su. Saboda haka kafin waccan doka ya kamata a gyara inda matsalar take tukunna

Comments
Post a Comment