Amnesty International Ta Yi Allawadai Da Kama Wanda Ya Hada Zanga-Zanga A Jihar Katsina.
Hukumar kare hakkin ɗan Adam ta duniya Amnesty International, tayi alawadai da kama Nastura Sharif, sakamakon jagorantar zanga-zangar lumana ga gwamnatin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Mai magana da yawun hukumar Isa Sanusi ne ya bayyana haka ta hanyar aikewa da jaridar Punch da sakon kar ta kwana, inda yace lallai ne gwamnatin tarayyar Najeriya da tayi saurin sakinsa.
Sanusi ya rubuta “dole ne hukumomin Najeriya su saki Nastura Ashir Sharif, saboda bai aikata komai ba face gaskiya da kuma kare rayukan al’umma”.
Yace ba abinda ya aikata face kiran gwamnati da tayi abinda ya dace, hakan na nuni da cewa Gwamnatin Buhari ta hana fadar ‘yancin baki da kuma ‘yan magana kamar yadda yake kundin tsarin mulkin ƙasar nan.


Comments
Post a Comment