Skip to main content

Posts

TAJBank: Empowering Lives Through Non-Interest Banking

TAJBank: Empowering Lives Through Non-Interest Banking By Sani Ahmad Giwa   In a world where many financial institutions are driven by profit at the expense of their customers, TAJBank stands tall as a beacon of trust, integrity, and innovation. TAJBank is not just another bank — it is a movement toward ethical prosperity, financial inclusion, and peace of mind. If you’re searching for a banking partner that truly cares about your growth, your values, and your future — TAJBank is the answer. Why TAJBank? Because You Deserve Better Here’s why thousands of Nigerians across the country are making the switch to TAJBank: ✅ Non-Interest Banking (Riba-Free): TAJBank operates on Islamic finance principles, meaning no interest is charged or paid. Your money works for you in a way that’s ethical, fair, and transparent — without hidden fees or exploitative charges. ✅ Ethics First: At the core of TAJBank is a strong moral foundation. This is a bank that honors honesty, transparency, and mutual...
Recent posts
Mulkin Buhari Annoba Ce Ga Mutanen Najeriya - Solomon Dalung Tsohon Ministan wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana jimamin sa kan kashe-kashen da ake yi a yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya da Arewa Maso Yamma. Dalung, ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo a shafinsa na Facebook inda ya bayyana bakin cikin shi game da yadda ake kashe ‘yan kasa a yankin Arewa duk da tsananin kashe kudin tsaro. Dalung yace an kashe yawancin yan Najeriya mazauna Arewa a karkashin kulawar Buhari fiye da kowane lokaci a cikin tarihi. Da yake magana da yaren Hausa, Dalung, wanda ya kasance minista a karkashin Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2019, ya bayyana tsarin mulkin a matsayin wanda ya gaza.           Talla Ya soki Shugaban kasar da laifin kyale jami’an tsaro su kwashe dukiyar al’umma ba tare da sakamako mai gamsarwa ba. Ya ce, “Ya Shugaba, ka ba wadannan mutane karin kudi, duk da haka muna ci gaba da asarar rayuka da dama. Wadannan mutane suna wadatar da ...
Amnesty International Ta Yi Allawadai Da Kama Wanda Ya Hada Zanga-Zanga A Jihar Katsina. Hukumar kare hakkin ɗan Adam ta duniya Amnesty International, tayi alawadai da kama Nastura Sharif, sakamakon jagorantar zanga-zangar lumana ga gwamnatin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Mai magana da yawun hukumar Isa Sanusi ne ya bayyana haka ta hanyar aikewa da jaridar Punch da sakon kar ta kwana, inda yace lallai ne gwamnatin tarayyar Najeriya da tayi saurin sakinsa. Sanusi ya rubuta “dole ne hukumomin Najeriya su saki Nastura Ashir Sharif, saboda bai aikata komai ba face gaskiya da kuma kare rayukan al’umma”. Yace ba abinda ya aikata face kiran gwamnati da tayi abinda ya dace, hakan na nuni da cewa Gwamnatin Buhari ta hana fadar ‘yancin baki da kuma ‘yan magana kamar yadda yake kundin tsarin mulkin ƙasar nan.
Tsaro: Za A Yi Zanga-Zanga A Arewacin Najeriya Kungiyar matasan Arewa karkashin jagorancin Alhaji Nastura Ahmad Shariff ta kira jama’ar arewacin Najeriya su fito suyi zanga zanga akan matsalar tsaro da ta addabi yankin a ranar Talata. Za a yi wannan zanga zanga ne a dukkanin jihohi goma sha tara na arewacin Najeriyar. Zanga zangar za ta kunshi kungiyoyin yan gwagwarmaya na farar hulla, kana za a watsa ta a kafafen sada zumunta. A baya bayan nan kuma dai harkar tsaro ta yi matukar gurbacewa a yankin Arewacin Najeriya musamman a jihohin Katsina, Sokoto da kuma Zamfara.
CORONA: BANKIN CBN YA WARE NAIRA BILYAN HAMSIN DOMIN TALLAFAWA MUTANE - Lai Mohammed Daga Sumayya Bashir Ministan yada labarai Mista Lai Mohammed ya ce babban bankin Najeriya CBN ya ware zunzurutun kudade har naira bilyan 50 domin tallafawa wadanda annobar cutar Corona ta tagayyara ta fuskar durkushewar kasuwancinsu, da kuma magidantan da suke cikin halin ha-ula'i. Lai Mohammed ya ce tuni dai bankin ya fara turawa da kudaden ta hanyar bankin 'yan kasuwa wato NIRSAL wanda ya dauki ragamar aikin don ganin an ba mutanen da suka dace, musamman kananan 'yan kasuwa da magidanta.
DOKAR FYADE: BA NAN GIZO KE SAKA BA Daga Sani Ahmad Giwa Fyade dai a Najeriya tun ba yau ba ya zama ruwan dare gauraye duniya, wanda kuma hukuma suka kasa daukan wani tsauraran matakai ga duk wanda ya aikata hakan akan kananan yara ko manya; inda lokuta da dama har wasu kungiyoyi ko masu hannu da shuni suke bai wa mutanen da suke aikata laifin fyade kariya ta hanyar daukar lauyoyi da makamantansu. Hakika wannan dabi'a ta sa guyawun iyayen yaran da aka lalata wa rayuwa yin sanyi wajen bin diddigin kwatar wa 'ya'yansu hakkinsu, haka suke hakura suna kai kokensu wajen Allah. Madallah da irin kokarin da majalisar dokokin kasa da na wasu jihohi suke yi na himmar samar da wata doka da za ta iya rage yawaitar wannan dabi'a ta fyade, kuma za ta tsoratar tare da razanar da masu sha'awar aikata hakan ga kananan yara ko manya. Kamar yadda yawancin membobin majalisar suka fi raja'a akan shi shi ne a zartas da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu cikakkiyar shaid...
JIBWIS Ta Yi Allah Wadai Da Kashe-Kashen Da 'Yan Ta'adda Ke Yi A Yankin Arewa. Kungiyar ta kuma umurci limaman juma'a da kamsul-salawat da suyi addu'oi a masallatai Daga Ibrahim Baba Suleiman Kungiyar wa'azin musulunci ta JIBWIS ta nuna alhininta da matukar damuwa akan kashe-kashen bayin Allah da basuji ba, basu gani ba da ake yi a Jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Borno da sauran su. Hakan ya fito ne daga bakin Shugaban JIBWIS Sheik (Dr) Abdullahi Bala Lau a wani zantawa da yayi da 'yan jaridu a maraicen asabar dinnan. Shehin Malamin ya nuna damuwarsa matuka akan kisan kiyashi da ake yi a yankin arewa maso gabar, da arewa maso yamma, ''Ina mika sako na musanman ga Gwammatin tarayya cewa wannan kashe-kashen da ake yi fa yayi yawa, koda rai guda ne wajibine Gwannati ta kare ballantana rayukan mutane masu yawa. Dole Gwamnati ta sake nazari domin tsare rayukan Jama'arta, tun mutane basu fara daukan makami domin kare kansu ba, wanda a ka...